ISTA'ILA TANA KAFA SHINGE A YANKIN FALASDINAWA

Babbar Kotun kasar Isra’ila tace dolene gwomnatin kasar bude wata hanyar zage da za’a bi daga inda take gina katangar shinge kanta daga yankin yammacin kogin Jordan. A yau Alhamis ne kotun Kolin kasar ta yanke wannan hukunci kan wata kara da Palasdinawa dake zaune a wani kauye suka shigar dake cewa wannan shinge da Isra’ila ke kafawa a gefen garin Qalqilya na yankin Palasdinawa, ta toshe musu hanyarsu ta zuwa wasu yankunan yanmmacin kogin Jordan din. wani kwamiti mai alkalan Isra’ila 9 daya saurari wannan karar yace Isra’ila tana da ‘yancin gina katanga a yankinta domin kare al’umarta daga hareharen ‘yan kunan bakin wake. Bara ne kotun duniya ta yanke hukunci cewa wannan katanga da isra’ila take ginawa baya bisa ka’ida.