Hankali Ya Fara Kwanciya A Maidugurin Jihar Borno

Harkokin yau da kullum sun fara komowa kamar yadda aka saba yau litinin a Maiduguri, a yayin da 'yan sanda da sojoji suke ci gaba da yin sintiri kwanaki biyu bayan da aka kashe mutane 15 a wata tarzomar da ta samo asali daga wani taron nuna kyamar zane-zanen batunci na Annabin Rahama.

Wasu Musulmi sun kai farmaki a kan Kiristoci da majami'u da kantuna na Kiristocin kafin 'yan sanda da sojoji su tarwatsa su a ranar asabar.

A jiya lahadi, babban sakataren Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya, Alhaji Lateef Adegbite, ya roki Kiristoci da kada su ce zasu nemi daukar fansa, yana mai bayyana wannan tarzoma a zaman danyen aikin jahilci da wasu Musulmi suka aikata duk da cewa abubuwan da suka yi ya sabawa addinin Musulunci.

Wani babban malamin addinin Musulunci a birnin na Maiduguri ma, Sheikh Muhammad Abba Aji, ya ce kuskure ne ga Musulmi su kai farmaki kan wadanda ba Musulmi ba domin wadanda suka tsokani Musulmi su na Denmark ne ba a Nijeriya ba. Ya ce duk wanda ya sanya hannu a wannan lamarin ba Musulmin kwarai ba ne.

Sheikh Abba Aji ya ce, "Wallahi ina mai tausayawa wadanda wannan abu ya same su, ina mai yi musu addu'ar Allah Ya canja musu (abinda suka yi hasara) da wani abinda ya fi wannan. Kuma Allah Ya ba su hakuri."

Ita ma kungiyar nan ta "Borno Muslim Forum" wadda ta shirya zanga zangar ta Maiduguri, ta tsame hannunta daga tarzoma da kone-konen da aka yi. Shugabanta, Alhaji Babagana Aji, ya ce yana son tabbatarwa da al'ummar Kiristoci a Jihar cewar babu yawu ko hannunsu a wannan aikin da ya ce na haramun ne.

Alhaji Babagana Aji ya ce hare-hare a kan wuraren ibadar Kirista ko kan mabiya wasu addinan da aka yi a Maiduguri, haramun ne domin ya sabawa dokokin Musulunci.