Mutane 47 ne aka kashe a kasar Iraq

Jami’an Iraq sunce akallan mutane 47 ne aka kashe sannan aka jiwa 148 rauni a wani jerin harin rokoki da bama bamai da aka kai jiya Lahadi a birnin Bagadaza. Jami’an sunce wasu fashe fashe har biyar a jere wadanda suka had da rokoki da bam da aka dana cikin motoci da kuma wani dan kunar bakin Wake da ya kwaso aguje kan Babur sun ragargaza wasu gine gine 2 dake dauke da akasarin ‘yan mazahabin Shia’a a anguwar Zafraniya a birnin Bagadaza. Tun da fari jiyan sojojin Amirka da na Iraq sun binciki ma’aikatar lafiya a birnin Bagadaza banyan da aka tsegunta musu cewa wasu ‘yan ina-da-kamu sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasar Iraq a ma’aikatar. Rundunar sojin amirkan ta ce ba wanda suka samu a ma’aikatar, duk da haka suna tsare da mutane 5 domin musu tambayoyi. A wani hari na dabam kuma, jami’an tsaron Iraq sun kame mantane 16 wanda sukace suna shirin kashe ‘yan uwan firayiminstan kasar Nouri Almaliki. Rundunar sojin amirka ta ce ta kama wani shugaban ‘yan gwagwarmaya wadanda ke da hannu a wani hari na ranar 17 ga watan jiya a cikin wata kasuwa a garin Mahmoudiyya da ya kashe mutane 50.