Koriya ta Kudu da Japan sun yi marhabin da shawarar Koriya ta Arewa, ta komawa ga shawarwarin kasashe da dama a kan shirinta na nukiliya, amma sun ce zasu ci gaba da aiwatar da takunkumin da aka kafawa Pyongyang a bayan gwajin nukiliyar da ta yi.
Mataimakin ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu, Yu Myung-hwan, yayi kashedi a yau laraba cewar za a sassauto da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kan Koriya ta Arewa ne kawai idan har aka samu ci gaba wajen kawar da shirin nukiliyar Pyongyang a tattaunawar da za a yi.
Shi ma kakakin gwamnatin Japan yayi irin wannan kashedi a birnin Tokyo, yana mai fadin cewa Japan zata ci gaba da yin aiki da takunkumin har sai an samu ci gaba a tattaunawar da za a yi.
A yau laraba Koriya ta Arewa ta ce zata koma kan teburin shawarwari muddin dai za a tattauna batun dage takunkumin kudi wanda Amurka ta sanya mata.