Ka fahinci dabarun kare kai daga cutar Murrar Tsuntsaye

KARANTA KAJI LABARI GAME DA CUTAR MURRAN TSUNTSAYE.

Ga bayanai masu fadakarwa game da cutar murrar tsuntsaye da cibyar tarayar da kasa da kasa ta Amirka USAID take so ku fahinci wannan cuta da kuma yadda za ku kare kanku da al’umar dake tare da ku.

Ga jerin matakai da ake son a dauka. Ka shirya gonarka ta kiwon tsuntsaye ko kaji. Ka tunafa yau ne ranar da ake so ka fara shirya kare kanka da gonarka daga illar ko annobar wannan cuta ta murran tsuntsaye.

Ka dauki lokaci mai tsawo wajen shirye kaji, da Agwagin da kake kiwo. Ka kebe kajinka waje guda tahanyar sasu cikin wani shinge. Ka rabasu da agwaji. Rarraba sabbin kyankyasa ko matasa daga tsoffi na akallan tsawon kwanaki 14. Ka raba musu wajen kiwo da dabbobi.

Ka share shinge, ka share gashin kaji akai-akai. Ka kula da tsaftace kayakin amfanin kaji a kullum rana. Zaka iya kare kanka da iyalanka ta hanyar wanke hannunka da sabulu ko toka bayan ka taba kaji ko kwansu. Kar ka manta ka goje takalmarka kafin ka fita daga cikin gonar kajinka.

Duk wani kokari da kayi na kare lafiyar tsuntsaye ka kare lafiyar dabbobi da na iyalinka da sauran al’umar dake yankin ne. A duk lokacin da kowa yayi aikinsa daidai, to zamu kara karfi wajen kula da lafiyarmu. Hadin kanmu na iya hana yadon cutar murrar tsuntsaye.