Shugaba Bush Ya Kara Kasashen Afirka Takwas Cikin Wadanda Zasu Ci Moriyar Shirin Yaki Da Maleriya

Shugaba Bush ya kara sunayen kasashen Afirka takwas cikin wadanda zasu ci moriyar wani shiri na rage yawan mace-mace daga cutar maleriya ko zazzabin cizon sauro da rabi.

Shugaban ya fada yau alhamis lokacin wani taron koli kan cutar da sauro ke yadawa a fadarsa ta White House cewar za a kara sunayen Jamhuriyar Benin da Ethiopia da Ghana da Kenya da Liberiya da Madagascar da Mali da kuma Zambiya cikin kasashen da zasu ci moriyar shirin da ake kira Shirin yaki da Maleriya na Shugaba.

Wannan shiri na shekara 5 zai samar da dala miliyan dubu daya da dari biyu wajen ayyukan rigakafi da warkar da cutar maleriya a kasashen Afirka. Kasashe bakwai dake cikin wannan shiri tun farko sune Angola, Tanzaniya, Uganda, Malawi, Mozambique, Rwanda da Senegal.

Tun fari a yau alhamis, uwargidan shugaban Amurka, Laura Bush, ta bayar da sanarwar wani sabon shirin dala miliyan talatin na taimakawa kungiyoyin jama’a a karkara wajen yaki da cutar maleriya a Afirka da kasashen nahiyar Amurka.

Har ila yau ta bayar da sanarwar cewa shugaba Bush zai ayyana ranar 25 ga watan Afrilun shekara mai zuwa ta 2007 ta zamo ranar fadakarwa kan cutar maleriya.

Fadar White House ta ce yara biyu suke mutuwa cikin kowane minti daya a sanadin zazzabin cizon sauro a nahiyar Afirka.