Hukumar Lafiya ta Duniya tace Ashirye take don yaki da annobar ..

Shugabar Hukumar Lafiya ta duniya tace kasahe dari da casa’in da biyu da suke cikin kungiyar sun dauki wani mataki na zama cikin shirin ko ta kwana, ko watakila a sami barkewar annobar mashassharar tsuntsaye a duniya.

Darekta Janar na Hukumar Margarate Chan ce ta ce ganin matakin da aka dauka wani ci gaba ne sosai idan aka kwatanta da yadda hali yake a shekarun baya lokacin da sai kasashe 50 kadai suka shirya don yaki da cutar a duniya baki daya.

Ms Chan tace ci gab da aka samu a kayakin ayyukan fasaha suna iya zama wasu hanyoyin tinkarar mammunar annobar cutar a duniya baki daya. Mammunan nau’in nan na cutar watau H5N1 akasari tana kama dan Adama a sakamakon taba kaji ko tsuntsaye da suka harbu da cutar. .

To amma wadandsu kwararru sunyi imanin cewa Kayayoyin cutar na iya rikida su zama masu yado tsakanin bani Adama. Cutar murrar tsuntsaye ta kashe mutane wajen 192 tun daga shekara ta dubu 2003 yawanci a kasashen Asiya.