An sami labarin bullar cutar Masassharar Tsuntsaye a Burma

Likitocin dabbobi a kasar Burma sun bada rahoton wani sabon bullar cutar mashassharan tsuntsaye yayin da suka gwada naman wadansu kaji guda biyu a wata gona dake kudancin kasar. Jami’an kasar sunce matattun kajin suna dauke da kwayoyin cutar nau’in H5N1.

Kasar Burma ta bada rahotannin bullar cutar a kasar a sau da yawa, saidai ba’a sami wani mutun da ya kamu da cutar a kasar ba. Mutane 192 ne suka mutu a sakamakon kamuwa da cutar tun shekara ta 2003 aklasarinsu a yankin kasashen Asia. Hukumar lafiya ta Duniya tace idan mutum yakusanci kaji ko tsuntsaye da suka kamu da cutar shima yana iya kamuwa da ita.