Lebanon Tace ta Kama 'Yan Leken Asirin Isra'ila - 2002-02-26

Rundunar sojojin kasar Lebanon tace dakarunta sun kame mutane uku da ake zargin suna yiwa Isra'ila ayyukan leken asiri.

A yau Talata ne rundunar sojojin ta bada sanarwar cewa an kame mutanen ne bayan wani binciken da aka gudanar, wanda ya fallasa aika-aikar gungun masu aikin leken asirin, da kokarinsu na bayarwa da Isra‘ila wasu muhimman bayanai kan tsarin ayyukan sojojin Lebanon da Syria da kuma wasu bayanai a kan yadda Hizbullah ke gudanar da ayyukanta.

Mutanen da ake zargi da laifin leken asirin sun yi kokarin bai wa Isra'ila bayanan ayyukan cibiyoyin hada-hadar kudaden Lebanon. Amma bayanin da rundunar sojojin ta Lebanon ta hayar bai bayyana lokaci da wurin da aka kame mutanen ba, kazalika ba'a san jinsun da suka fito ba.