MDD Ta Shawarci Kwango-Kinshasa Da Ta Girka Sojoji A Bakin Iyakarta... - 2002-05-03

Wata tawagar Kwamitin Sulhun MDD da take ziyarar nahiyar Afirka a yanzu, ta gabatar ad shawarar cewa ya kamata kasar Kwango-Kinshasa ta girka sojoji a bakin iyakarta, domin kare kasashe makwabtanta daga hare-haren 'yan tawayen dake buya cikin Kwangon.

Shugaban wannan tawaga ta MDD, jakada Jean-David Levitt na Faransa, shine ya bada wannan shawara a lokacin da suka ziyarci kasar Angola a jiya alhamis.

Shawarar tayi kiran da a girka rundunar hadin guiwa ta Rwanda da Kwango a kusa da bakin iyakar ita Kwangon da Rwanda. Har ila yau, sojojin Kwango Kinshasa zasu yi aiki tare da takwarorinsu na Uganda da Burundi wajen kafa rundunonin hadin guiwa a iyakokinsu.

Rwanda da Kwango-Kinshasa sun yi marhabin da wannan shawara.

Hare-hare daga tsallaken iyaka da 'yan tawayen Rwanda da Burundi da kuma Uganda suke kaiwa cikin kasashensu daga Kwango, na daya daga cikin musabbabin yakin basasar kasar Kwango Kinshasa.