MDD Ta Kara Wa'adin Aikin Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya A Birnin Kabul - 2002-05-24

Ba tare da wata hamayya ba, Kwamitin Sulhun MDD ya jefa kuri'ar kara watanni shida a wa'adin aikin sojojin kiyaye zaman lafiya dake birnin Kabul a kasar Afghanistan.

Amma kuma Kwamitin ya ki yarda da kiran da shugaban gwamnatin rikon kwarya Hamid Karzai yayi, na a fadada ayyukan sojojin kiyaye zaman lafiyar zuwa wasu biranen na kasar Afghanistan.

Amurka ce ta gabatar da kudurin kara wa'adin aikin sojojin kiyaye zaman lafiyar su dubu 4 da 600. A ranar 20 ga watan Yuni ne wa'adin watanni shidan farko na rundunar zai kare.

A halin da ake ciki, hukumomin Afghanistan sun sako fursunoni 'yan Taleban su fiye da 500 daga wani gidan kurkukun da ya cika makil a yankin arewacin kasar. Ana tura fursunonin zuwa birnin Kabul a cikin motocin safa.

Wani kakakin ma'aikatar tsaron Amurka, ya shaidawa Muryar Amurka cewa jami'an sojan Amurka ba su da wata damuwa game da sako wadannan fursunoni da aka yi.