Turawa Manoma Akalla Biyar Zasu Gurfana Gaban Kotu Jumma'a A Zimbabwe - 2002-08-15

An umurci turawa manoma su akalla biyar a kasar Zimbabwe da su bayyana a gaban kotu gobe Jumma'a, a saboda sun ki bin umurnin gwamnati na ficewa daga cikin gonakinsu.

Sune na farko da zasu gurfana a gaban kotu, daga cikin dubban turawa manoman kasuwanci da suka ki bin umurnin gwamnati na ficewa daga cikin gonakinsu, domin a rarraba wadannan gonaki ga bakar fatan da ba su mallaki filayen noma ba, a karkashin shirin gwamnati na sake rarraba filayen kasar.

Lauyoyin da suke wakiltar manoman sun ce zasu kalubalanci wannan umurnin a saboda su a ganinsu ya sabawa tsarin mulki.

Idan aka samu manoman da laifi, ana iya yanke musu tara, ko kuma a daure su a gidan kurkuku na tsawon shekaru biyu.

A ranar laraba, wasu bakaken fata 'yan kama wuri zauna, sun fara tilasta yin aiki da umurnin ficewa daga cikin gonakin, inda suka fatattaki wani manomi da iyalansa daga cikin gonarsu.