Fada Ya Barke A Kusa Da Babban Birnin Kasar Ivory Coast - 2002-10-01

Fada ya barke a tsakanin sojojin 'yan tawaye da na gwamnati a kusa da Yamoussoukro, babban birnin kasar Ivory Coast.

Wannan fada da ake yi a Tiebissou, mai tazarar kilomita 40 a arewa da babban birnin, ya zo a daidai lokacin da ake samun rahotannin cewa sojojin 'yan tawaye sun kama karin wasu yankunan arewacin kasar. Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce 'yan tawayen sun kwace garin Sakassou jiya litinin da daddare.

Faransa zata aike da karin sojojin laima guda 70 domin kafa hedkwatar tsara dabarun yaki a Abidjan, cibiyar cinikayya ta kasar, a shirye-shiryen yiwuwar kafawa da tura rundunar sojojin kwantar da hayaki ta Afirka ta Yamma. Sojojin Faransa da tuni suke kasar Ivory Coast sun kafa sansanoni a yankunan dake tsakanin Yamoussoukro da Bouake, birni na biyu wajen girma a kasar, wanda kuma ke hannun 'yan tawaye.

Wakilan kungiyar ECOWAS masu shiga tsakani da suka gana da shugaba Laurent Gbagbo a jiya litinin, suna kokarin ganawa da 'yan tawaye.

An kafa wannan tawagar ministocin harkokin waje daga kasashen Nijeriya da Ghana da Togo, a lokacin taron gaggawar da aka yi na Kungiyar ta Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma ranar lahadi a Accra, babban birnin Ghana.

Shugabannin ECOWAS sun bayyana goyon baya ga shugaba Gbagbo, sun kuma ce zasu tura runduna ta sojoji dubu 4 zuwa Ivory Coast idan har kokarinda ake yi na sasantawa ya ci tura.

Wannan fitina ta barke ranar 19 ga watan Satumba a lokacin da sojoji kimanin 700 suka yi bore a sassa dabam-dabam na kasar.