Wata Girgizar Kasar Ta Sake Ratsa Kasar Italiya - 2002-11-01

Wata sabuwar girgizar kasa mai karfin gaske a kudancin kasar Italiya ta sa an kwashe mutanen kauyen San Guiliano di Puglia, inda a jiya alhamis wata girgizar kasar ta kashe mutane 29, akasarinsu yara kanana.

Cibiyar Nazarin Halittar Kasa ta Italiya ta tabbatar da cewa an sake yin girgiza fiye da sau guda a yau Jumma'a da tsakar rana. Daya daga cikin girgizar ta kai awu 5 da digo 3 a ma'aunin motsin kasa na Richter, watau karfinta yayi kusan girgizar jiya alhamis.

Masu aikin agaji sun kawo karshen binciken da suke yi na wadanda ke da rai a cikin wata makarantar da ta rusa a kauyen. Jami'ai sun ce yawan mutanen da suka mutu a girgizar kasa 29 ne, cikinsu har da yara kanana 26 wadanda suka hada da wani aji baki daya na yara 'yan shekaru shida-shida. Sauran ukun kuwa wani malami ne a makarantar, da wasu mata tsoffi biyu da suka mutu cikin gidajensu.