Batun Zaben Nigeria: Wata Kungiya ta yi kashedi. - 2003-04-10

Wata Babbar kungiyar kare hakkokin bil adama ta ce tarzomar siyasa a Nigeriya na yin mummunar barazana ga babban Zaben da za a fara a kasar a gobe Asabar.

A Cikin wani rahoto daga gabatar a jiya alhamis, kungiyar Human Rights Watch ta ce mummunar zanga-zanga na iya barkewa a kasar bayan da aka kammala zagaye na ukku na zaben a ranar 3 ga watan Mayu domin mayar da martanin duk wani mataki da ake ganin na magudin zaben ne.

Wannan Kungiya mai Hedkwata a birnin New York ta kuma roki gwamnatin Nigeriya da jami'an Zabe da 'yan sanda da su yi kokarin ganin sun samar da yanayin da za a karfafa guiwar jama'a ga tsarin zaben kasar.

Kungiyar ta ce akasarin manyan laifuffukan siyasar da aka aikata a kasar ba a hukumta kowa ba, al'amarin dake nuna kamar masu aikata irin wadannan laifuffuka da magoya-bayansa kan tsira ba tare da an hukumta su ba. Haka kuma Kungiyar ta ce kisan gilklar siyasar da aka ringa aikatawa a 'yan kwanakin nan da kuma fadan kabilancin da aka ringa yi sun kara fargabar da ake ta karuwar tarzomar siyasa a lokacin Zaben.

A cikin wannan Rahoto, Human Rights Watch ta bukaci hukumomin Nigeriya da su hukumta duk wadanda aka samu da laifin siyasa da sauran laifuffukan keta hakkokin jama'a. Ta kuma bukaci gwamnatocin kasashen waje su ci gaba da iza wuta akan gwamnatin ta Nigeriya domin ganin ta gurfanar da irin wadannan mutane a gaban Kuliya.