Libya Tace Tana Fatar Kyautata Dangantakarta Da Amurka - 2003-08-17

Libya ta ce tana fatar daukar alhakin da ta yi na dasa bam a jirgin saman da ya tarwatse a samaniyar Lockerbie a shekarar 1988, zata kyautata dangantaka a tsakaninta da Amurka.

A cikin hirarrakin da suka yi asabar da kafofin yada labarai na kasashen yammaci, jami'an Libya sun bayyana kwadayin yin aiki tare da Amurka.

A ranar Jumma'a Libya ta rubuta takardar da a ciki ta dauki alhakin dasa bam din da ya tarwatsa jirgin saman kamfanin Pan Am mai lambar tafiya 103, ta kuma yarda zata biya diyyar tsabar kudi dala miliyan dubu 2 da 700 ga iyalan mutane 270 da suka mutu a sanadin wannan lamari.

Amma kuma Libya ta ce ba zata biya karin diyyar ko kwabo ba ga iyalan mutanen da suka mutu a sanadin bam din da aka dasa cikin wani jirgin saman Faransa a 1989, duk ad cewa Faransa ta yi barazanar zata toshe duk wata kafar dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanyawa Libya idan har ba ta kara kudin diyyar ba.