Harin Bam Na Ta'addanci Ya Kashe Babban Limamin Shi'a Na Iraqi - 2003-08-30

Wani harin bam na ta'addanci da aka boye cikin mota a birnin Najaf mai tsarki ga 'yan Shi'a a Iraqi, ya akshe mutane 75, cikinsu har da Ayatollah Mohammed Baqir al-Hakim, daya daga cikin manyan shugabannin 'yan Shi'a masu rinjaye a Iraqi.

Wannan bam na jiya Jumma'a ya raunata mutane akalla 140 a lokacin da ya tashi daidai lokafin da masallata suke tashi daga sallar Jumma'a a Masallacin Imamuna Ali. A lokacin hudubar Jumma'ar, Ayatollah Hakim yayi rokon da al'ummar Iraqi su hada kansu.

Wannan babban limami yana hada kai da sabuwar majalisar mulkin Iraqi, kuma ya kyale magoya bayansa suna shiga cikin ayyukan sake gina kasa.

Shugaba Bush ya yi tur da wannan harin a zaman mummunan ta'addanci. Ya ce sojojin Amurka za su taimaka wajen farauto wadanda suke da hannu a wannan lamarin.

Babban sakataren MDD, Kofi Annan, yayi tur da harin bam din, ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin Iraqi da su guji ayyukan tayar da fitina haka nan. Ya ce Iraqi zata samu zaman lafiya da kwanciyar hankali ne kawai idan har aka shimfida tsarin siyasa na gaskiya da zai kunshi kowa da kowa.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin, amma wasu magoya bayan Ayatollah Hakim suna dora laifin a kan magoya bayan saddam Hussein. An ganawa Ayatollah Hakim azaba a zamanin mulkin Saddam, aka kuma tilasta masa yin gudun hijira zuwa Iran na shekaru 20.

Wasu 'yan Iraqin suna dora laifin wannan hari a kan kungiyar al-Qa'ida, ko kuma sauran kungiyoyin Shi'a ko na Sunni masu adawa da ta su.