Harin Bam Na Baya-bayan Nan Ya Kashe Mutane 4 A Iraqi - 2003-10-29

Harin bam na baya-bayan da aka dasa cikin mota a kasar Iraqi ya kashe mutane akalla hudu a yamma da birnin Bagadaza, a yayin da shugaba Bush na nan Amurka yake dora laifin wadannan hare-hare a kan magoya bayan Saddam Hussein da 'yan ta'addar kasashen waje.

'Yan sandan Iraqi da kuma shaidu sun ce motar dake shake da bam din ta yi bindiga jiya talata a Fallujah, kimanin mita 100 daga wani caji ofis na 'yan sanda.

A halin da ake ciki kuma, rundunar sojojin Amurka ta ce an kashe sojan Amurka guda ranar litinin a birnin Bagadaza, a lokacin da aka cilla masa gurneti.

Har ila yau, hukumomin taron dangin da Amurka take yi wa jagoranci sun bayar da sanarwar cewa an bindige aka kashe mukaddashin magajin garin birnin Bagadaza, Faris al-Assam, a kusa da gidansa ranar lahadai da daddare. Daga baya a jiya talata, an bindige aka kashe wani dan jarida dan kasar Iraqi a Mosul.

Shugaba Bush dai ya ce hare-haren zi-da-zuci da ake kaiwa kan fararen hula ba za su karya wa Amurka kwarin guiwa ba.