An Kammala Taron Kolin Shugabannin Afirka Ta Yamma Kan Rikicin Ivory Coast - 2003-11-12

Shugabannin wasu kasashe bakwai na Afirka ta Yamma sun roki Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da ya duba yiwuwar kara karfin rundunar kiyaye zaman lafiyar majalisar a kasar Ivory Coast.

A cikin sanarwar da suka bayar a karshen taron kolin wuni guda da suka gudanar jiya talata a Accra, babban birnin kasar Ghana, shugabannin sun ce ana bukatar wannan runduna domin karfafawa, daga baya kuma domin maye gurbin wata runduna ta sojojin yankin dake kasar ta Ivory Coast a yanzu haka.

Har yanzu kasar Ivory Coast tana rabe, watanni hudu a bayan da aka cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar watanni 10, wanda ya barke a sanadin tawayen da bangaren arewacin kasar yayi.

Kungiyar ECOWAS, wadda ta dauki alhakin taron na Ghana, tana da sojoji kimanin dubu 1 da 500 a Ivory Coast, a bayan sojojin Faransa su dubu 4 wadanda ke lura da bakin iyakar da aka shata a tsakanin sassan masu yakar juna.

A jiya talata, babban sakataren MDD, Kofi Annan, yayi gargadin cewa idan ba a gaggauta sake hade kasar ba, zaben da aka shirya gudanarwa a shekarar 2005 ba zai yiwu ba.

A bayan shugaba John Kuffour na Ghana da shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast, taron ya samu halartar shugabannin kasashen Togo, Nijar, Burkina Fasso, Nijeriya da kuma Benin.