Alkaluma A Manyan  Kasuwannin Saida Hannayen Jari A Turai Da Asiya Duk Sunyi Kasa A Hada Hadar Yinin Litinin

Babu wata ribar da aka samu a cinikayyar hannayen jarin da aka gudanar a kasuwannin turai bayan an buɗeta da hantsi zuwa tsakar rana, sannan a kasuwannin shunkun Asiya can ma ba’a kai wani labari ba.

Farashin man fetur kuma na ci gaba da yin ƙasa duk da sanarwar da ƙungiyar OPEC ta bayar na rage yawan man da ake haƙowa. Masu zuba jari na ci gaba da nuna damuwa da yadda tattalin arzikin ƙasa da ƙasa ke ci gaba da tafiyar Wahainiya duk da matakan da Gwamnatocin ƙasashen ke ɗauka domin bunƙasa tattalin azrikin.

Alƙaluman hannayen jari na Nikkei a Japan sun yi ƙasa da kashi 26 daga cikin ɗari duk da sanarwar da Gwamnatin Japan ta bayar na ɗaukan matakin tallaffawa kasuwar shunkun da kuɗaɗe domin sayen hannayen jari. Hannayen jari na CAC a Kasuwar Paris faransa sun yi ƙasa da kashi biyar daga cikin ɗari, kazalika hannayen jari na DAX a kasuwar Farnkfurt Jamus sun yi ƙasa da kashi uku daga cikin ɗari.