An Haramtawa Shugabannin Mulkin Soja A Nijar Takara A Zabe Da Zasu Shirya Nan Gaba

Sabon shugaban mulkin sojin jamhuriyar Niger yace an haramtawa kusoshin gwamnatin mulkin sojan tsayawa takara a zaben da gwamnatin ta alkawarta gudanarwa.

Kakakin gwamnatin mulkin sojan Col, Abdulkarim Goukoye ya shaidawa manema labarai jiya Laraba cewa za a gudanar da zabe nan gaba, duk da yake ba a tsaida lokacin gudanar da shi ba. Gwamnatin mulkin sojan ta zabi PM farin kaya da zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe.

Rundunar soji ta hambare gwamnatin shugaba Mamadou Tandja makon jiya, bayan ya jefa kasar cikin rudamin siyasa bara a kasar mai arzikin uranium ta wajen sake kundin tsarin mulkin kasar da nufin ci gaba da mulki. Hambararren shugaban kasar da manyan ministocinsa suna ci gaba da kasancewa karkashin daurin talala.

Kakakin mulkin sojan ya bayyana cewa kasar Morocco tayi tayin ba shugaba Tandja mafaka sai dai ba a yanke hukumci kan makomarsa ba.