Jigon Siyasa A Iraq Ya La’anci Girke Dakarun Kasashen Waje Har Abada

Wani babban jigon Jam’iyyar ‘Yan Shi’a, mai mulkin kasar Iraq, yayi watsi da yiwuwar kafa wani sansanin sojojin kasashen waje na din-din-din a kasar.

Ammar al Hakim, mutum na biyu mafi tagomashi a cikin jam’iyyar, yayi bayanin ne a jiya, a wata huduba da ya gabatar wajen Sallar Idul Fitri, wacce ta kawo karshen azumin wata guda da musulmi suka yi.

Yayi kiran da al’ummar Iraki su hada kai, su kuma guji kashe kashen juna. Yace lallai ne a kafa jamhiriya mai larduna dake da ikon cin gashin kansu, domin a samar da cikakken hadin kan da zai taimakawa shimfida tabbataccen zaman lafiya a kasar.

Yace Al’ummar Iraqi sun fara daukar matakan hade kawunansu, kuma zasu iya cimma nasara ne kawai idan makasudin wannan hadin kai ya kasance gina kasa da warware matsalolinta. Ammar al Hakim ya wakilci mahaifinsa ne, Sheikh Abdulaziz al Hakim, Shugaban Babbar Majalisar Islama ta Iraq, wanda ke fama da cutar sankara.

Shekaranjiya Juma’a wani tsohon Kwamandan Rundunar Sojin Amurka a Iraq, Janar Ricardo Sanchez ya chaccaki Gwamnatin Shugabab Bush, saboda rashin iya gudanar da yakin Iraq yadda ya kamata, har ma yace yakin ya zame wa Amurkawa kamar wani mugun mafarkin da bashi da ranar karewa.