Kungiyoyin Hamayya  A Iran Suna Kira Da A Yi Zanga Zanga Ranar Bikin Yujin Juya Hali

Kungiyoyin masu hamayya a kasar Iran sun bukaci ayi zanga zanga a bikin kewayowar ranar da kasar ta kaddamar da juyin juya hali . Sakoni da hotunan vidiyo da aka sa a shafunan dandalin gizo a jiya litinin, sunyi kira ga magoya bayan masu hamaiya da suyi jerin gwanon nunawa gwamnati rashin amincewa, a ranar sha daya ga watan fabrairu.

Daya daga cikin hoton vidiyon ya nuna iyawar masu hamaiya na ci gaba da yin zanga zangar ko kuma gangamin nuna rashin amincewa duk da yunkurin da jami’an tsaro ke yin na dakile wannan aniya tasu. An gabatar da wannan kira ne duk da barazanar da gwamnatin kasar tayi na ladabtar da duk wanda ya tada zaune tsaye a ranar da Iran ke dauka da muhimmancin gaske.

A halin da ake ciki hukumomin kasar suna yiwa mutane biyar shari’ar bisa zargin rawar da suka taka a zanga zangar kin jinin manufofin gwamnati da aka yi a watan disamba.