Nouri Al-Maliki Ya Fara Yunkurin Dinke Barakar Da Ya Yiwa Gwamnatinsa

An gaiyaci manyan ‘yan Shi’a da Sunni da kuma Kurdawan kasar zuwa wajen wannan taro da za a gudanar a birnin bagadaza.

Jami’an kasar Iraqi sun gaya wa manema labarai cewar za a tattauna muhimman al’amura da suka shafi yarjejeniya kan kafa gwamnatin hadin gambiza.

A jiya Litinin Tsohon Prime Minista Ayad Allawi, wanda a halin yanzu yake jagorancin wani bangare na majalisar kasar, ya sahidawa gidan rediyon NPR ta nan Amurka cewa Mr. Maliki yana daya daga cikin masu ta’azzara rikicin kasar, kuma wani sulhu da nufin farfado da harkokin siyasar kasar zai yi wuya, in dai ba wata sabuwar gwamnati aka kafa ba, wacce zata yiwa ‘yan kasar adalci.

A jiyan dai Rundunar Sojin Amurka tace ta kaddamar da wani sabon farmaki, da nufin murkushe tsagerun ‘yan Ahlul Sunna da na ‘Yan Shi’a.