A yau Litinin Shugaban Amurka mai jiran gado, Barack
Obama ya yabi mai fafutukar kwatar 'yancin dan adam dinnan na Amurka, Martin
Luther King Junior, saboda fifikon da ya bayar kan aikin jama'a.
Yau ranar hutu ce a nan Amurka, wadda aka ware domin
karrama Martin Luther King, wadda kuma ake amfanim da ita wajen karfafa guiwar
aikin gayya.
A jiya Lahadi ma, Obama ya halarci bukukuwan share
fagen kaddamar da shi a matsayin Shugaban Kasa na 44, inda ya kai ziyara zuwa
makabartar soji domin karrama sojojin da suka sadaukar da rayukansu ga Amurka.
Daga baya kuma ya halarci wani bikin kade-kade da
raye-raye da dubban mutane suka halarta.