Sojojin Najeriya Sunyi Arangama Da Tsagerun Niger Delta

Sojojin Nigeria sun tarwatsa gungun 'yan yakin sa-kai na Niger Delta da suka so kai hari akan gidajen ma'aikatan wani kamfanin man fetur.

Jami'an tsaron sunce a jiya Talata ne wadanan mayakan su kamar 20, dauke da makamai kuma a cikin jiragen kwale-kwale masu dan karen gudun tsiya, suka abkawa wannan gidan da ke zaman mazaunin ma'aikatan kamfanin man fetur naExxon Mobil dake Eket a jihar Akwa Ibom.

Jami'an suka ce sun share kamar mintoci 30 suna gwabazawa da mayakan, amma sanarwar kamfanin ExxonMobil din tace ba wanda aka kashe. Hare-hare irin wadanan akan mazaunun ma'aikatu ko kamfunnan man fetur dai abu ne da aka saba das hi sosai a wannan yankin na Niger delta, wanda kamar shine hedkwatar irin wadanan bata-garin.

A inda aka fiton nan, anfi yawan samun irin wannan tashin hankali a jihohin Rivers da Bayelsa, amma a kwanan nan, masu kai harin sun tsanata yawan tada kayar baya a izuwa sassan dake can wajajen inda Nigeria da Cameroon suka yi kan iyaka.

A kwanan baya ne babbar kungiyar 'yan yakin sa-kai ta Niger Delta din, MEND, tace ta janye yarjejeniyar tsagaita wutar da ta kulla da hukumomi, bayanda tayi zargin cewa soja sun kai hari akan wata maboyarta.