A Gasar Champions Dai, Babu Kamar Real Madrid

Real Madrid La Liga

Bisa yadda Atletico Madrid take kallon lamura yanzu, abunda kawai zai shiga tsakaninta da season din da bata taba yin irinshi ba a tsawon kungiyar na shekaru 111, itace bakar ‘yar adawarta dake cikin birnin daya da ita wato Real Madrid.

A tarihi, wadannan kungiyoyin Spain guda biyu sune na farko a cikin kungiyoyin dake birnin daya, wadanda suka samu nasarar kaiwa wasan karshe na Champions wanda za’a doka a birnin Lisbon.

A gasar Champions dai, babu kamar Real Madrid, kuma ta share shekaru 12 tana jiran ta cinye kofin a karo na 10. A kwanakin baya idan ba’a manta, Atleticon a karon farko a cikin shekaru 14 ta buge Real a kofin Copa del Rey wanda aka yi a filin wasan Santiago Barnabeu.

Jami’an tsaro na binciken tsohon Kocin Manchester United, ana zarginshi da kaiwa wani mutum duka a wani wajen nishadi.

Wannan lamari dai ance ya faru ne tsakanin Moyes mai shekaru 51 da mutumin mai shekaru 23 Alhamis dinnan, a arewacin Ingila.