Majalisar Dinkin Duniya ta ware watan Oktoban, kowace shekara, a matsayin watan wayar da kan mata akan cutar sankaran Nono.
Dangane da haka ne Dandalin VOA, ya samu tattaunawa da wani likita, a asibitin, Malam, Aminu dake Kano, Dr. Abdulrahaman Abba Sheshe, inda ya bayana mana cewa a shekaran da ta gabata an yiwa mata tamanin da uku,Tiyatar Nono saboda cutar sankara.
Yace idan aka kwatanta da shekaran da ta gabata kuma za’a ga cewa an samu karuwan masu dauke dawannan cutar, yace gano cutar da wurin yana taimakawa wajen yin magani.
Dr. Abba Sheshe, yace abinci mai maiko da yawa, na iya jawo sankara, kuma mutane masu kiba, suma, suna da barazanar kamuwa da wannan cutar.
Ya kuma kara da cewa cutar sankaran Nono, tafi kama mutane daga shekaru goma sha biyar zuwa shekaru arbain da biyar, amma yace masamman, daga shekaru talatin da biyar zuwa arabain da biyar an fi samun masu dauke da cutar.
Yakara da cewa masu shekaru kasa ko kuma fiye da haka suma suna iya kamu da cutar, yace sankaran Nono, har maza ma suna iya kamuwa da ita.
Your browser doesn’t support HTML5
Sankaran Nono - 3'30"