Akwai Bakin Haure Miliyan 3 da Dubu 700 Masu Ilimin Jami’a, a Amurka.

An yi kiyasin cewa akwai kimanin bakin haure miliyan 3 da dubu 700 masu ilimin Jami’a, a Amurka.

A Wani bincike da kungiyar aiyukan ilimi, na duniya mai zaman kanta,ta gudanar da taimakon gidauniyar James Knight, an gano cewa kashi 26 cikin 100 na wadannan bakin hauren basu aiki ko kuma suna kananan aiyuka wanda ko kusa bai dace da ilimin su ba.

Mataimakiyar Shugaban, gidauniyar James Knight, Carol Coletta, ta ce gidauniyar, ta samarda tsabar kudi dala dubu 70 domin gudanar da wannan binciken wanda shine irinsa na farko, da aka gudanar da zamar gano bakin haure masu ilimin Jami’a.

Ta ce idan aka yi amfani da ilimi da kwarewar wadannan bakin masamman a birane da aka gudanar da binciken , kamar Detroit, Miami, Philadelphia, Califonia, Boston da Seattle, toh tabbaci hakika,zai taimaka gaya ga tattalin arzikin biranen.