Akwai Bukatar Sake Dabarar Shawo Kan Lamarin Boko Haram

'Yan bangan Fararen Hulan JTF suna anfani ne da kulake da sanduna da makaman da aka sarafa cikin gida suna sintiri a kan titunan Maiduguri, Najerya.

Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara, masana harkar tsaro sun ce ya kamata a sauya dabara game da batun murkushe Boko Haram
A yayin da aka doshi shiga sabuwar shekara, masana harkar tsaro a Najeriya sun yi waiwayen baya domin nazarin inda aka kwana game da batun samar da tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar.

Dr. Bawa Abdullahi Wase, masani kan harkar tsaro, yace ya kamata Najeriya ta yi koyi da irin abubuwan da suka wakana a kasashe dabam-dabam na duniya game da yakar ta'addanci, musamman ma a kasar Afghanistan, inda a bayan yakin shekaru kimanin goma, Amurka da kawayenta suka rungumi batun tattaunawa domin kawo sulhu.

Dr. Wase, yace babu ta yadda za a iya kawo karshen wannan lamarin ta irin matakan da gwamnatin Najeriya take dauka, domin ba zasu taba wadatarwa ba a irin wannan lamarin, tilas sai an hada da neman yin sulhu, ko ana so ko na a so.

Haka kuma, ya bayarda shawarar da a biya diyyar wadanda suka rasa rayukansu ko dukiyoyinsu a sanadin wannan yaki da ake yi da 'yan Boko Haram, a kuma dauki matakan tallafawa wadanda aka musgunawa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola...

Your browser doesn’t support HTML5

Masana Sun Ce Da Sakel Game Da Sha'anin Tsaro - 3'20"