Masu neman a dage zabe a kwai masu munmunan manufa, a wanin bangaren kuwa wasu suna son hakan ne don wasu dalilai masu mahinmanci matuka. A cewar shugaban sashen wayar da kan jama’a na hukmar zabe Barr. Olowale Ozi, yace wasu dagacikin jam’iyyu da suka nemi a dage zabe ba sun yi hakan don wata manufa bane, illa don neman a samu ingabtaccen zabe a kasar, amma wasu kuwa suna son hakan ne don su samu damar da zasu muzguna ma jama’a.
Tun bayan biyowar furucin me baiwa shugaban kasa shawara a harkar tsaro wato Kanal Sambo Dasuki mai murabus, da yanemi da a dage zaben da aka shiryar za'a gudanar a ranar sha hudu ga wannan watan na fafrairu, wanda ya jawo cecekuce a kasar. Mr. Ozi dai ya nuna cewar hukumar su a shirye take ta gudanar da zaben a wannan ranar da aka shiryas.
A wani bangaren kuma ‘yan adawa naganin wanna zai maida hannun agogo baya ne don suna gani kamar wannan gwamnatin na shirin yi wani abune a wanna tsarin, tabakin Sanata Hadi Sirika, yace su bazasu yar da dawannan bukatar ta shugaban kasaba idan ma aka kawo musu to za suyi kunnen uwar shegu da ita ne kawai. Don a matsayinsu na masu wakiltar al’uma bazasu bari a sa al’uma Najeriya cikin mawuyacin haliba.