Al-Shebab tace zata ci gaba da kai hare-hare kan Uganda

  • Aliyu Mustapha
Kungiyar ‘yan kishin Islama ta Somalia ta Al-Shebab tace zata ci gaba da auna Uganda da hare-haren ta’addanci don nuna rashin amincewarta da tarbaccen sojan da Uganda ke bayarwa ga Rundunar Sojojin Afrika dake Somalia.

Madugun kungiyar ‘yan kishin Islamar nan ta Somalia da ke ikrarin cewa itace ta kai farmakin ta’addancin da aka kai kwanan nan a Uganda, yace kungiyar tasu na shirin kai karin irin wa’anan hare-haren. Shiekh Muktar Abu Zubayr ya fito ta gidajen rediyo a yau Alhamis, a can Mogadishu, yana godewa ‘yan kunar bakin waken da suka cinna ta’asar kashe mutane 70 yayinda suke kallon kwallon kafar gasar cin kofin duniya ta telebijin a Kampala, babban birnin na Uganda. Abu Zubayr yace kungiyar al’Shebab zata ci gaba da daukan ramuwa akan Uganda saboda sojan da Uganda ta tarbata ga Rundunar Sojojin Afrikan dake aikin kawo sulhu a nan Somalia. Sai dai kuma, a nasa murtanin, shugaban Amurka Barack Obama, ya nuna jin takaici da wannan harin, musamman na ganin yadda kungiyoyin dake da alaka da Al-Qaida suka soma kasashen Afrika. Shugaba Obama yace muddin ba burki aka ja wa kungiyoyi irin na al-Shebab ba, to ba’a san irin barnar da zasuyi a sauran kasashen waje ba.