WASHINGTON, DC —
An bukaci jama’a, da suyi amfani da lokacin bukukuwan Kirsimeti, wajen kawo zaman lafiya da fahimtar juna, wani shugaban aluma, dake yankin Mubi, a jihar Adamawa, Alhaji Abama Kwaccham, ne ya furta haka a wani hira da wakilin muryar Amurka, Ibrahim Abdulazeez.
Ya kuma yi kira ga Musulmi da Kirista, da su zauna lafiya domin a cewarsa duk masifar da ta fadawa garuruwansu, duk da Musulmi da Kirista ya shafa, saboda haka yace hada kai tsakanin addinai ya zama wajibi.
Alhaji Kwaccham, ya kara da cewa hada Musulmi da Kirista, a kasar daya da Allah yayi, yayi ne domin ya nuwa karfin mulkinsa saboda haka ya zama tilas mu zauna da juna domin haka Allah yaso shi yasa ya yimu a kasa daya amma mabiya addinai daba-daban.