An ci gaba da yin garambawul a ma'aikatar mai ta Nigeria

Ofishin NNPC a Abuja-Nigeria.

Kwana daya bayan da shugaban Nigeria Mohammadu Buhari ya nada sabon shugaba a ma'aikatar mai ta Nigeria, an ci gaba da yin garambawul a ma'aikatar.

Kwana daya daya bayan an nada sabon shugaba a ma'aikatar mai ta Nigeria, an ci gaba da yin garambawul a ma'aikatar, inda aka salami manyan direktocin ma'aikatar su takwas.

Wata takarda mai dauke da sa hannun sabon shugaban ma'aikatar man fetur ta Nigeria, Emmanuel Idekechukwu, yayi bayanin sunayen mnyan direktocin ma'aikatar da aka salama wadanda tsohon shugaba Goodluck Jonathan ne ya nada su a 2014.

Wakiliyar sashen Hausa Medina Dauda ta aiko da rahoton cewa tuni har masu ruwa da tsaki a harkar man fetur suka fara tofa albarkacin bakin su a gameda sauye sauyen da aka yi a ma'aikatar man fetur.

Abubakar Mai Dandi, shine mataimakin shugaban kungiyar dilalan mai ta kasa. Yace canjin da aka yi, yayi daidai, domin yace sabon shugaban ma'aikatar mai da aka nada zai shiga taitayinsa, domin ya tabbatarda cewa idan aka yi wani abinda ba daidai bane, to shima komai yana iya faruwa a gare shi.

Abubakar Mai Dandi ya yi kira ga sabon shugaban ma'aikatar da yayi kokarin kwatanta gskiya. Ya kuma tabbatar cewa ya bi umarnin doka da oda kamar yadda shugaban kasa yace so.

Haka kuma yace ya kamata inda ake adana mai da suke da mai, kuma dayake su dilalan mai su biya kudadensu, a tilasta musu su sayar da mai akan farashin da aka tsayar, domin suma dilalan mai su saidawa talakaaa akan farashi.

To amma kuma duk da wannan yunkuri, mutane suna fargabar kada a koma gidan jiya na karancin mai.

Your browser doesn’t support HTML5

Garambawul a ma'aikatar man Fetur ta Nigeria 3'39"