An Gano Kirar Motar Da Aka Yi Amfani Da Ita Wajen Kai Hari A Kano - 19/5/2014

NIGERIA - Karin bayan daga harin bom a Kano ya nuna cewa an gane irin kirar motar da akayi amfani da ita wajen kai harin. Wani babban jami’in soja da ya tattauna da Muryar Amurka ya bayyana cewa anyi amfani da motar ‘Toyota Sienna’ ne wajen kai harin.

NIGERIA - Mai fashin baki akan al-amuran yau da kullum Kabiru Lawanti yana kallon taron da shuwagabannin Faransa, da Najeriya, da Kamaru, da Chadi da Nijar sukayi a matsayin wani sabon salo da turawan mulkin mallaka suke amfani dashi wajen gani cewa sun rage irin katsalandan da sukeyi a kasashen Afirka. Wato, a maimakon shiga da sojojinsu suyi maganin rigima, yanzu sun koma aikin bayarda shawarwari.

NIGERIA - Yayinda ake cigaba da kokarin ceto daliban Cibok, hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta kai tallafin kayayyakin abinci ga al-ummar Cibok, wadanda yanzu haka suke fama da matsalar rashin abinci, yayin da shiga yankin keda wahala saboda matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin.