An Gano Wani Sinadari Dake Hana Yaduwar Cutar Daji

Tambarin wayar da kan jama'a kan cutar daji

Masana sun gano cewa wani sinadari da ake amfani da shi wajen hana abinci lalacewa, yana kuma hana yaduwar wani nau’in cutar daji.
Masana a jami’ar Michigan sun gano cewa wani sinadari da ake amfani da shi wajen hana abinci lalacewa, yana kuma hana yaduwar wani nau’in cutar daji da take kama mutane a kai da kuma wuya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa sinadarin da ake kira “Nisin” a turance, yana sa wani abinci mai gina jiki kashe kwayoyin cutar Kansa, amma baya illa ga jikin bil-Adama da bashi da cutar.

Nau’in cutar daji da take shafar bakin mutum da ake kira “Oral Cancer” tana kan gaba wajen janyo mace mace a fadin duniya, inda kamar kashi 40-60 na wadanda aka gano sun kamu da cutar suke rayuwa na tsawon shekaru biyar.