An Sake Jin Karar Fashe-fashe da Harbe-Harbe Yau Asabar a Maiduguri - 15/03/2014

Mutane sunyi dafifi kewaye da inda boma-boman ya tashi a Maiduguri a ranar 14 ga watan Maris 2014.

Za a yi aiki da dokar hana fita waje daga 9 na dare zuwa 6 na safiya a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno

Hankulan mutanen dake zaune a kewayen barikin Giwa na Maiduguri sun sake tashi yau asabar da safe a bayan da aka ji karar harbe-harbe da fashe-fashen nakiyoyi.

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu, yace da misalin karfe 8 na safiyar yau aka fara jin karar harbe-harben, sannan daga bisani aka yi ta jin karar fashe-fashe a yayin da jiragen saman yaki ke shawagi a sama.

Mutanen dake zaunea kusa da barikicin sun arce a saboda rade-radin cewa watakila 'yan Boko Haram da suka tsira daga harin jiya Jumma'a ne suka sake komowa.

A wani gefen kuma, gwamnatin Jihar Borno ta kafa dokar hana fita waje idan ba na ma'aikatan gaggawa ko 'yan jarida ba, daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safiya. Sakataren gwamnatin jihar, Baba Ahmed Jidda, shi ne ya bayyana wannan cikin wata sanarwar da ya aikewa da 'yan jarida.

Har yanzu dai babu kiyasi na yawan wadanda suka mutu, amma akwai majiyoyin tsaron da suka ce ba a taba samun nasara tare da yin barna ma 'yan ta'adda kamar a wannan karon ba.