Ana Adawa da David Moyes - 3/29/14

Lokacin da David Moyes yake Coach din Everton.

To fa an shirya wani jirgi, ya tashi dauke da wani katon kyalle wanda ke neman coachin kungiyar Manchester, David Moyes ya sauka daga mukaminsa, a dai-dai lokacin fara wasan Firimiya tsakanin Manchestan da Aston Villa a filin Old-trafford. A jikin kyallen an rubutu “Bai Iya Ba – Moyes ya tafi”.

Sir Alex Ferguson shine ya zabi Moyes da hannunsa, amma gashi wannan season din da kyar ManU take bin Tottenham dake matsayin ta 6 a teburi da maki 5, kuma wasanni bakwai ne kacal suka rage a Firimiyan.