Ana Iya Bada Kariya a Loakcin Zabe Tunda Anbada a Lokacin Yakin Kanfe

Zabe

Bisa cigaba da korafe korafe da mutanen Najeriya keyi dangane da dage zabe. Yau mun samu tattaunawa da shugaban wata kungiyar matasa Komarat Abdulmajid Babangida Sa’ad, wanda yayi muna karin haske dangane da nashi hasashen, da yasa hukumar zabe me zaman kanta ta dage zaben, daga inda aka shiryar dashi.

Yace yana gani wannan bawani abu bane illa dai ita hukumar zaben na kokarin biyan bukatun jam’iyya mai mulki, kuma wannan wata damace da su ‘yan jam’iyya me mulki su samu damar yin magudi. Don haka wannan bai kamata ace ita hukumar na daukar umurnin gwamnati me ci ba sabo da ita hukumace me zamankanta.

Komarate Babangida, dai ya kara da cewar ai da rashin tsaro ne zai sa a dage zabe, to ya akayi shi shugaban kasa yaje wadannan jihohin don yakin neman zabe, kuma jami’an tsaro suka bashi kariya da ta kamata. Ashe Kenan zasu iya ba ma al’umar wannan yanki kariya don a gudanar da zabe yadda yakamata. Yana dai ganin wannan bai yi daidai da tsarin demokaradiyya ba.

Ya kara da cewar yakamata kasashen duniya suyi tir da irin wannan kamakaryar da akeyi ma demokaradiyya, su kuma samar da wani horo me tsanani ga duk kasa da tayi irin wannan kashin mumuke ga demokaradiyya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kariya Lokacin Zabe - 3.01"