Kungiyoyin fararen hula, kugiyar kwadago da sauran shuwagabanin al’uma, na kira da a fara daukan sabbin Sojoji, ko a fadada binciken dalilan dake sanya rashin nasara a faggen daga, dake jawo galaba kan Sojojin, har ya kai ga kwace kauyuka, a arewa maso gabas.
Jami’an gwamnati, irin mai tamakawa shugaban kasa kan hulda da jama’a Mr.Doyin Okupe, a can baya yace don fadan sari ka noke ne yake jawo jinkirin rashin nasaran yakin.
Sai dai yanzu da ya kai ga kwace yankuna amsar ka iya shan banban, domin mukandashin Sifeto janar din ‘yan sanda, Suleman Abba, yace har yanzu ana neman kusan ‘yan sanda ashirin da suka bace a Gwoza yayin gumurzun kwace garin, inda ake da cibiyar horas da ‘yan sandan kwantar da tarzoma.
Sojojin dai na korafin cewa manyan sun a babakere kan kudadensu na alawus, wanda hakan ke hanasu kuzari a faggen daga.
Sai dai kakakin Sojojin Manjo Janar Chris Olukolade, yace ya musanta zargin,yace wannan shaci fadi ne kawai ana biyan Sojoji, a faggen daga nan take.
Your browser doesn’t support HTML5
Sojoji - 3'00"