Jam'iyyar APC Tayi Babban Kamu

APC

Dan takarar neman shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta APC, janar Muhammadu Buhari, ya kai ziyarar yakin neman zabe a Jihar Neja.

Janar Buhari, dai wanda ya samu tarba daga dubban jama’a, ya sha alwashin tabbatar da ingantuwar tsaro, da samar da aikin yi a tsakanin ‘yan Najeriya, idan har aka zabe shi a babban zabe mai zuwa.

Jam’iyyar APC, tayi babban kamu a jihar ta Neja, mataimakin Gwamna Alhaji Ahmed Musa Ibeto, da wasu magoya bayansa da dama sun canja sheka daga PDP, zuwa APC, a daidai lokacin da janar Buhari ke kawo ziyara.

A jawabin sa akan dalilan canja sheka kuwa Musa Ibeto, yace jam’iyyar PDP, bata yin adalci ba, a zaben fidda gwani, kuma sun kai korafinsu ga uwar jam’iya, amma babu abun da aka yi.

Da yake maida martani Gwamna Babangida Aliyu, yace” duk wanda Allah yaba mu shine namu amma muna rokon shi cewa duk wanda zai zamo mana cikas Allah ga kawar mana dashi kuma munga Allah na karbar rokon mu don mun soma gani sun fara kaucewa.”

Your browser doesn’t support HTML5

Canja sheka -2'49"