Atletico Madrid Da FC Barcelona Sun Tashi Kunnen Doki A Karon Giwayen Lig Na Spain - 1/4/2014

Neymar yana gaisawa da shugaba kungiyar FC Barcelona lokacin da aka saye shi.

Atletico Madrid ta bi FC Barcelona har gida a Camp Nou ta so ta doke ta a zagayen farko na wasan kwata fainal da suka gwabza a dazun nan, amma dai Barcelona ta tsamo kitse a wuta.

Diego Ribas dan kasar Brazil ya jefa ma Atletico kwallo a raga cikin minti na 56 da fara wasa, inda magoya bayansu da suka biyo su har Barcelona suka barke da ihun murna cikin fili.

A cikin minti na 71 da fara wasa kuma, Neymar na Bracelona ya karbi kwallo daga kafar Iniesta, ya narka a cikin raga, ya rama wa masu masaukin baki.

Daga nan 'yan Barcelona suka mike suka fara kai hare-hare, amma haka aka tashi da ci daya da daya.

Kungiyoyin biyu zasu sake karawa da juna a ranar 9 ga wata.