Duniyarmu A Yau

Yan matan Indiya sun yi kwalliyar awarwaro masu kala daban daban don kasancewa a cikin shagalin murnar zagayowar ranar 'yancin kasar a tagwayen biranen Secunderabad da ke Hyderabad

Sarki Akihito (Hannun Dama) da Sarauniya Michiko sun rusuna a dakin taro na Budokan dake birnin Tokyo ranar bikin cika shekaru 72 da mika wuyan Japanawa a lokacin yakin duniya na biyu don girmama mamatan da yakin ya lashe.

Nan wani Gleidson Hoffman ne dan asalin kasar Brazil ya kasa daurewa har ya fashe da kuka lokacin da ake bikin da aka yi a birnin New York na rantsar da baki 30  daga kasashen duniya 19 da suka zama Amurkawa.

Wani manomi a lokacin da yake ratsa wasu gonakin noman shinkafa a gundumar Sindhuli ta kasar Nepal.

Wasu membobin kungiyar 'yan uwantaka na faman juya wata katafariyar wainar kwan da aka fashe kan kwayaye guda  dubu 10 akan farantin soya kwai guda 1 a wani bikin gargajiyar toya wainar kwai a garin Malmedy na kasar Belgium.

Wani kwado mai kyakkyawan launi na shakatawa a wani gulbi da ke gidan ajiyar namun daji na Leipzig ta kasar Jamus.

Indonesian paratroopers descend with their chutes during the Jalak Sakti military exercise held at the Sultan Iskandar Muda Air Force Base in Blang Bintang, Aceh province.