Babban Bankin Najeriya Ya Bada Umurnin Ci Gaba Da Amfani Da Tsofaffin Kudi

Your browser doesn’t support HTML5

Bayan shiru na wasu kwanaki tun bayan hukuncin kotun kolin kasar, babban bankin Najeriya ya umurci bankuna a kasar da su ci gaba da mu’amala da tsofaffin takardun kudi na naira 200, da 500 da dubu daya har zuwa karshen wannan shekara.