Bam Ya Sake Tashi A Nyanya, Abuja Dazun Nan - 1/5/2014

Mutane sun taru a inda Bom ya fashe a tashar motar haya ta Nyanya, kilomita 16 daga tsakiyar birnin Abuja, Najeriya, Afrilu 14, 2014.

Rahotanni daga Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya na fadin cewa an sake samun tashin wani abu kamar bam a Nyanya, daura da inda bam ya tashi kwanakin baya ya kashe mutane akalla 70.

Har yanzu babu wani cikakken bayani na wannan sabon bam da ya tashi a kusa da tashar motar hayar ta Nyanya.

A kasance da DandalinVOA domin jin cikakken bayanin duk abinda ya faru game da wannan lamarin.