Barca da Atletico Zasu Yi Karon Battar Karfe!!! - 1/4/2014

La Liga a Spain

A daya wasan na yau, FC Barcelona zata karbi bakuncin Atletico Madrid. Wadannan kungiyoyi biyu, sune suke saman La Liga na Spain, kuma maki daya tak ya raba tsakaninsu.

A karawar da suka yi sau uku a wannan shekarar dai babu wadda ta iya doke wata daga cikinsu, duk a kunnen doki suke tashi.

Atletico Madrid tana gadara da dan wasanta Diego Costa wanda yayi ta jefa mata kwallaye a bana, amma kuma kungiyar da ya kasa jefa kwallo a ragarta, ita ce Barcelona.

Tana yiwuwa kuma ragar ‘yan barcelona ta yi rawa, domin kuwa mai tsaron gidanta na daya, Victor Valdes, ba zai buga wasa ba.