Basussukan Da Najeriya Ke Karbowa Na Raya Kasa Ne - Malam Garba Shehu

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan adawa da wasu masu fashin baki suna ci gaba da sukar gwamnantin Najeriya bisa yawan basussukan kasashen waje da take karbowa.
A baya bayan nan shugaban Najeriya ya sake bukatar majalisar dokokin kasar da ta amince da ya karbo bashin dala biliyan hudu daga kasashen waje. Sai dai a hira da Muryar Amurka a Washington DC, kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce akwai abin da mutane ba su fahimta ba a game da wannan bashi.