Bauchi Ta Kara Inganta Aikin Rigakafin Polio

An Samu Tazara A Yaki Da Polio A Jihar Bauchi

An inganta yadda ake bayarda maganin rigakafin Polio a Jihar Bauchi saboda yaran dake shigowa daga makwabtan jihohi inda cutar ta yi tsanani
Hukumar kula da lafiya tun daga matakin farko ta Jihar Bauchi, ta fadada yadda ta ke bayarda maganin rigakafin kamuwa da cutar shan inna ko Polio, ganin yadda ake samun bakin dake komawa jihar daga wasu jihohi makwabta inda al'amuran tsaro suka hana gudanar da ayyukan bayarda rigakafin.

Dr. Nisser Aliyu Umar, shugaban hukumar, yace a bana, babu inda cutar Polio ta yi tsanani kamar yankin Arewa Maso Gabas, musamman a saboda rashin kwanciyar hankali a jihohin dake wannan yanki. Yace jihohin Borno da Yobe, inda aka fi fama da fitina, nan ne kuma cutar ta fi tsanani.

Amma Dr. Umar yace an samu sabbin kamuwa da cutar Polio guda 4 a Jihar Bauchi ya zuwa wannan lokaci a cikin shekarar nan. Yace a dalilin haka ne ya sa yanzu a kowane wata, ma'aikatan asibiti a Jihar su kan shiga cikin garuruwa da kauyuka su kakkafa tebura su na bayar da maganin rigakafin, maimakon su jira har sai lokutan da ake kaddamar da kyamfe na yaki da wannan cuta.

Ya ja kunnen ma'aikatan hukumar dake bayarda wannan maganin da su kasance masu mutunta jama'a da halin kwarai, yana mai rokon jama'a da su ba da jami'an hadin kai domin raba Jihar Bauchi da ma Najeriya da wannan cuta ta Polio.

Wakiliyarmu Amina Abdullahi Girbo, ta aiko da karin bayani kan wannan.

Your browser doesn’t support HTML5

Dr. Nisser Aliyu Umar Kan yaki Da Polio A Jihar Bauchi - 3:57