Bom ya Fashe A Jos

Jos Blast, Najeriya ( File Photo)

Misalin karfe shida da rabi ne agogon Najeriya, boma-boman suka fashe a babbar kasuwar birnin Jos dake arewacin Najeriya.

Wakiliyar Dandali Zainab Babaji ta samu bayanai dake cewa a kalla mutane 7 ne suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ya dauki alhakin harin, amma a baya-bayannan an zargi kungiyar tayar da kayar baya, Boko Haram da kai hare-hare a duk fadin arewacin Najeriya.