Bom Ya Fashe A Kano

Kano, Najeriya. (File Photo)

Mun sami labarin fashewar wani bom a kusa da wata kasuwa da ranar nan a birnin Kano.

Shugaban kasuwar kantin kwari Alhaji Liti Kululkul shen ya fadi hakan amma bai bada karin bayani ba.

Haka kwanan nan aka kai hari a masallaci a babban birnin garin, abinda ake kyautata zato 'yan kungiyar Boko Haram ne, inda suka tada boma bomai uku suka kuma budewa wa danda keyin ibada a masallacin wuta.